17 Satumba 2020 - 09:58
An Bayyana Lokacin Zaben Raba Gardama Kan Sabon Kundin Tsarin Mulkin Kasar Aljeriya

Shugaban kasar Algeria ya sanya hannu a kan doka wacce ta bada damar a gudanar da zaben raba gardama na sabon kundin tsarin mulkin kasar a ranar 1 ga watan Nuwamba mai zuwa.

ABNA24 : Jaridar al-Qudsul Arabi ta nakalto labarin cewa shugaba Abdulmajid Tabun ya sanya hannu kan dokar, sannan ya bukaci dukkan ‘yan Algeria wadanda suka cancanci bayyana ra’ayinsu da su fito don yin haka a ranar daya ga watan Nuwamba, wato ranar da kasar ta sami ‘yancin kanta daga hannun turawan Faransa ‘yan mulkin mallaka a shekara 1962.

Muhimman al-amuran wadanda aka gabatar a cikin sabon kundin tsarin mulkin kasar dai sun hada da samar da kujerar mataimakin shugaban kasa, bawa Firai minister damar yin ayyukansa cikin walwala, da kuma bawa sojojin kasar damar gabatar da ayyuka a kasashen wanje a karon farko.

Kuma a ranar 20 ga watan Satumba da muke ciki ne za’a fara binciken sunayen wadanda suka cancanci bayyana ra’yinsu har na mako guda.

Jam’iyyun adawar kasar dai suna ganin gyaran da aka gabatar ba zai kawo sauyin damocradiyya da suke bukata a kasar ba.

342/